Jagororin jam’iyyar ADC suna gudanar da wata zanga-zanga a yau ranar Laraba a Abuja, inda suka nuna rashin amincewa da wasu matakai da Hukumar Zaɓen Najeriya ta ɗauka, waɗanda suka ce na barazana ga dimokuraɗiyya da kuma ‘yancin jam’iyyun adawa.
Zanga-zangar da aka yi wa take da #OccupyINEC ta haɗa manyan ‘yan siyasa da tsofaffin ‘yan takarar shugaban ƙasa, ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso da Rotimi Amaechi da Rauf Aregbesola da Aminu Tambuwal da kuma Dino Melaye.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun riƙe allunan goyon baya ga Sanata David Mark, suna bayyana amincewarsu da shugabancinsa a cikin jam’iyyar.
Da yake jawabi a madadin jam’iyyar ADC da sauran ‘yan adawa, Peter Obi ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su tashi tsaye domin kare dimokuraɗiyya, yana mai gargadin cewa bai kamata ƙasar ta koma tsarin jam’iyya ɗaya ba.
Ya ce duk masu kishin ƙasa su haɗu wajen kare haɗin kai da zaman lafiya.
Zanga-zangar ta biyo bayan matakin da Hukumar Zaɓen Najeriya ta ɗauka na daina kallon bangarorin jam’iyyar ADC guda biyu da Sanata David Mark da Nafiu Bala ke jagoranta, bayan hukuncin kotun daukaka ƙara kan rikicin shugabancin jam’iyyar.
ADC da wasu jam’iyyun adawa sun bayyana matakin a matsayin katsalandan a harkokin cikin gida na jam’iyya.