Rahotanni da ke fitowa daga ƙasar Kuwait sun nuna cewa wasu jiragen sojin Amurka da dama sun yi hatsari a safiyar yau, a cewar ma’aikatar tsaron Kuwait.
Sai dai babu wanda ya mutu, sannan an garzaya da waɗanda lamarin ya shafa zuwa asibiti don duba lafiyarsu.
Ma’aikatar tsaron Kuwait ta ce tana aiki da takwararta ta Amurka don binciken lamarin, kuma suna ci gaba da bincike don gano abin da ya janyo hatsarin.
Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da rikici ke bazuwa a yankin Gabas ta Tsakiya, inda Iran ke far wa sansanonin sojin Amurka a ƙasashen ƙetare a matsayin ramuwar gayya bayan farmakin da Amurka da Isra’ila suka kai wa Iran.