Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi na II, da Aminu Ado Bayero sun jagoranci Sallar Idi a wurare daban-daban a birnin Kano, yayin da tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, shi ma ya gudanar da nasa Sallar a keɓantaccen wuri, lamarin da ya nuna ƙara tsananta rabuwar kai a jihar.
Rahotanni sun ce kowanne ɓangare ya gudanar da Sallar ne tare da mabiyansa, abin da ya saba da yadda aka saba gudanar da Sallar Idi a Kano a matsayin wuri ɗaya da ke haɗa jama’a.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa Kwankwaso ya gudanar da Sallar ne a masallacin gidansa da ke Miller Road, tare da manyan magoya bayansa ciki har da mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdussalam Gwarzo da wasu tsofaffin jami’an gwamnati.
Mai magana da yawun Kwankwaso ya ce an gudanar da Sallar cikin yanayi na godiya da haɗin kai, tare da addu’o’i ga zaman lafiya.
Wannan rarrabuwar Sallar Idi na da alaƙa da rikicin sarautar Kano da ya daɗe yana ci gaba tun bayan cire Muhammadu Sanusi na II a 2020 da kuma mayar da shi kan karagar mulki a 2024, wanda ya haifar da samuwar sarakuna biyu masu ikirarin sarauta.
Baya ga rikicin sarauta, ana danganta ƙarin rarrabuwar kai da sauye-sauyen siyasa a jihar, musamman bayan sauya sheƙar gwamna Abba Kabir Yusuf daga NNPP zuwa APC, lamarin da ya sake raba ‘yan siyasa gida biyu.