An sako wani mutum mai shekaru 61, Kenneth Windley, daga gidan yari na Brooklyn, New York, bayan ya shafe kusan shekaru 19 ana tuhumar shi da sata da aka tabbatar bai aikata ba daga baya.
Windley ya fara zaman kurkuku tun shekara 2007, bisa hukuncin shekaru 20, sai dai daga baya wadansu shaidu sun tabbatar cewa ba shi ne ya aikata laifin ba, kuma babban lauyan kotun, Eric Gonzalez, ya ce an yi kuskure a shari’ar.
An kama Windley ne bayan wani lamari na takardar kudi da aka sace, amma baya da hannu a satar.
Windley ya bayyana cewa yana fatan komawa ga rayuwarsa da iyali.