Kotu ta sauke shugaban karamar hukumar Kumbotso, Ghali Basaf daga kujerarsa tare da ayyana Ali Musa Dan maliki a matsayin halastaccen shugaban karamar hukumar.
Bayanai sun bayyana cewa, a sake bankado wannan batu ne sakamakon jinkirin Ghali Basaf na yin mubaya’a ga gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf tun bayan komawarsa jam’iyya mai mulki ta APC.
Kafin zama shugaban karamar Kumbotso, Ghali shi ne shugaban kungiyar Kwankwasiyya Reporters na kasa, ya kuma kasance guda cikin hadiman tsohon gwamnan jihar Rabi’u Musa Kwankwaso.
Tuni aka gudanar da bikin rantsar da Ali Musa a fadar gwamnatin jihar karkashin jagorancin shugaban majalisar dokokin jihar, Hon Isma’il Falgore.
Matakin rantsuwar ya biyo bayan hukuncin wata kotu a jihar ta Kano da ya tabbatar da Musa a matsayin halastaccen shugaban karamar hukumar ta Kumbotso.