Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Kusan mutum 2,000 aka kwantar a asibiti a Isra’ila tun bayan ɓarkewar yaƙi da Iran

Ma’aikatar Lafiya ta Isra’ila ta ce aƙalla mutum 1,929 ne aka kwantar a asibiti tun bayan barkewar yaƙi da Iran, ciki har da 157 a cikin awanni 24 da suka gabata.

Ma’aikatar ta ce daga cikin waɗanda aka kwantar, mutum tara na cikin mawuyacin hali, yayin da 42 suka samu matsaƙaitan raunuka, sannan 70 kuma suka ji ƙananan raunuka.

Ta yi bayanin cewa mutane da dama sun ji rauni ne yayin da suke sauka zuwa wuraren mafaka, domin kare kansu daga hare-haren makamai.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use