Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Kuwait da Saudiyya sun kara haɗa kai kan tsaron bayan Hare-haren Iran

Shugabannin ƙasashen Kuwait da Saudiyya sun sake jaddada niyyarsu ta ƙarfafa haɗin kai wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin Gulf, bayan jerin hare-hare da Iran ta kai a kwanakin baya.

Sarkin Kuwait, Sheikh Mishal Al-Ahmad Al-Sabah, ya tattauna ta wayar tarho da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, inda suka tattauna matakan da za a ɗauka don kare yankin daga barazanar tsaro.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kuwait ya ruwaito cewa shugabannin biyu sun bayyana kudurinsu na yin duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.

A baya-bayan nan, an samu jerin hare-hare daga Iran da suka kai hari kan cibiyoyin makamashi a ƙasashen Gulf, ciki har da Saudiyya, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), da Qatar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use