Tsohon dan takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya fice daga jam’iyyar NNPP.
Madugun darikar Kwankwasiyya ya ce ya bar jam’iyyar ce saboda a yanzu ya samu wata wacce zai shiga domin makomar siyasarsa a zaben 2027 da ke tafe.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta a yau Asabar jim kadan bayan komawarsa birnin Kano.
A yanzu ana sa ran Kwankwason zai koma jam‘iyyar adawa ta ADC a gobe Litinin kamar yadda wata sanarwa da kungiyar darikar Kwankwasiyya ta fitar a ranar Asabar, ta nuna.
Tsohon gwamnan na Kano ya ce a yanzu, ya zama dole a sama wa ‘yan kasa mafita.
A baya dai anyi ta rade-radin komawar tsohon gwamnan jam’iyyar ADC, tun bayan ganin fuskokin wasu jiga-jigan jam’iyyar a bikin Sallah da aka yi a jihar Kano wadanda suka hada da tsohon dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar Labour, Peter Obi da gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde da kuma wasu kusoshin jam’iyyar NNPP.
A ranar Juma’ar da ta gabata ma an hangi Kwankwason da sakataren jam’iyyar ADC Ra’uf Aregbesola da kuma ziyarar da ya kai wa tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a Abuja.