Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Kwankwaso ya koma jam’iyyar ADC a hukumance

Kwankwaso Kwankwaso
Kwankwaso ya ce ya zama tilas a sama wa ‘yan Najeriya mafita (Kwankwaso/X)

Madugun ɗarikar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da komawa jamʼiyyar ADC tare da ɗimbin magoya bayansa a hukumance.

Kwankwaso ya bayyana haka ne yayin wani taro da aka gudanar a gidansa da ke Kano.

Tsohon gwamnan na Kano ya kuma buƙaci mabiyansa da su yi rajista da jam’iyyar ta ADC, domin shirya fafatawa a zaɓukan ƙasar da ke tafe.

A ranar Lahadi, Kwankwaso ya sanar da ficewa daga jam’iyyar NNPP, inda ya ce ya zama tilas a sama wa ‘yan Najeriya mafita.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use