Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Lakurawa sun kashe masallata biyar a jihar Kebbi

Masallata biyar sun mutu yayin da wasu uku suka jikkata a wani harin ramuwar gayya da ake zargin ‘yan ta’adan Lakurawa suka kai a wani masallaci a ƙauyen Dadin Kowa, na ƙaramar hukumar Maiyama a jihar Kebbi, yayin da suke tsaka da sallar tarawihi a daren Laraba.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bashir Usman, ya bayyana cewa harin na ramuwar gayya ne bayan wani yunƙurin kwantan ɓauna da bai yi nasara ba kan rundunar sojin Najeriya.

Lakurawa sun shahara wajen kai hare-hare a arewacin Kebbi da Sokoto, satar dabbobi, da tilastawa mazauna yankunan biyan haraji.

Rahotanni daga AFP sun ce adadin mutanen da suka mutu ya kai goma, yayin da bincike ke ci gaba wakana

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use