Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Lebanon ta haramta ayyukan Hezbollah bayan harin Isra’ila

Lebanon Lebanon
Wani gini da aka lalata a harin da Isra’ila ta kai kudancin Lebanon (EPA)

Firaministan Lebanon Nawaf Salam ya fitar da wata sanarwa yana mai cewa an haramta ayyukan soji da tsaro na Hezbollah, sa’o’i bayan da Isra’ila ta mayar da martani ga hare-haren rokoki da jiragen sama marasa matuki da kungiyar da ke da alaka da Iran ta kai kudancin Beirut.

Nawaf Salam ya ce duk ayyukan Hezbollah “haramtattu ne” kuma ya yi kira ga jami’an tsaro da su dakile duk wani hari da ya fito daga yankin Lebanon”.

Hezbollah da ke kawance da Iran ta tabbatar da cewa harin nata na ɗaukar fansa ne kan kisan da aka yi wa Jagoran Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei, tare da kare Lebanon da mutanenta”.

Sai dai, tuni Isra’ila ta mayar da martani ta hanyar kai hare-hare a babban birnin Lebanon, Beirut, tare da kashe mutum sama da 30  da kuma raunata wasu 149, a cewar kamfanin dillancin labarai na ƙasar.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use