Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Ma’aikatan asibiti sun jikkata a harin Isra’ila a kudancin Lebanon

Marasa lafiya da ma’aikatan asibiti sun jikkata yayin da Isra’ila ta kai hari a kudancin Lebanon

Wasu ma’aikatan lafiya da marasa lafiya sun jikkata sakamakon wani harin sama da Isra’ila ta kai a kudancin Lebanon, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Sanarwar da Asibitin Jami’ar Sheikh Ragheb Harb da ke Toul, kusa da garin Nabatieh, ta fitar ta ce harin ya lalata wasu muhimman sassa na asibitin, ciki har da sashen kula da marasa lafiya masu matsanancin hali (ICU).

Rahotanni sun nuna cewa jikkatar ta faru ne sakamakon shaƙar hayaki bayan harin ya auka kan wani gini da ke makwabtaka da asibitin.

Mahukuntan asibitin sun bayyana harin a matsayin take dokokin ƙasa da ƙasa, tare da cewa ya jefa rayuwar marasa lafiya da ma’aikatan lafiya cikin haɗari.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use