Majalisar wakilan Amurka ta kammala tare da miƙa rahoton binciken da ta yi kan zargin kashe Kiristoci a Najeriya.
Rahoton, wanda kwamitocin kula da kasafin kudi da harkokin waje suka hada, ya biyo watanni na bincike mai zurfi, zaman sauraron bahasi a majalisa da kuma ziyarar sa ido a Najeriya.
Rahoton ya mayar da hankali kan zarge-zargen musgunawa mabiya addinin Kirista da kuma karuwar hare-haren masu tsattsauran ra’ayi a wasu sassan Najeriya.
Mika rahoton ya zo ne bayan shugaba Trump ya sake ayyana Najeriya a matsayin kasar da za a saka wa ido dangane da take hakkin addini.
Haka kuma, ya umarci dan majalisa Riley Moore tare da shugaban kwamitin kasafin kudi, Tom Cole, da su jagoranci bincike kan tsanantawa Kiristoci da hare-haren ta’addanci.
Dan majalisa Moore ya tabbatar da mika rahoton ga Trump a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya bayyana ganawar da aka yi a fadar White House a matsayin gagarumin aikin hadin gwiwar jam’iyyun siyasa biyu.
A cewarsa, binciken ya kunshi zaman tattaunawa na sirri da kuma tura tawagogin ‘yan majalisa sau biyu zuwa Najeriya domin tattara bayanai kai-tsaye.