Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da bukatar Shugaba Bola Tinubu na samun bashi daga kasashen waje na dala biliyan 6 domin cike gibin kasafin kudi.
Rahoton ya fito ne daga kwamitin bashin cikin gida da na waje na majalisar, karkashin shugabancin Aliyu Wamakko, wanda ya duba bukatun shugaban kasar.
Tinubu ya nemi dala biliyan 5 daga Bankin Abu Dhabi don tallafawa kasafin kudi da biyan bashin da ake biya.
Haka kuma, ya nemi dala biliyan 1 daga Citibank na tarayyar turai domin gyaran tashoshin jiragen ruwa, wanda suka hada da tashar jirgin ruwa na Lagos da Tin Can.
Bayan karanta bukatun, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya mika wasikun zuwa kwamitin da ya bayar da rahoton, wanda ya kai ga amincewar Majalisar a ranar Talata.