Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Majalisar Dattawan Najeriya na zaman gaggawa kan dokar zabe

Majalisar Dattawan Najeriya za ta gudanar da zama na gaggawa a yau Talata, sakamakon ƙaruwar ce-ce-ku-ce kan gyaran dokar zaɓe, musamman tanade-tanaden da suka shafi tura sakamakon zaɓen ta intanet.

An sanar da wannan zaman gaggawan ne a cikin wata sanarwa da Akawun Majalisar Emmanuel Odo, ya fitar bisa umarnin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio.

‘Yan Najeriya na ci gaba da neman ayi musu bayani kan abin da dokar da aka yi wa kwaskwarima ta kunsa lamarin da ya sa suka fara zanga-zanga a Abuja daga ranar Litinin.

Ana sa ran zaman na yau Talata zai mayar da hankali ne kan bukatun jama’a kan dokar zaben.

A jiya ne dai aka hangi al’umma da dama suka fito rike da alluna a bakin kofofin shiga zauren majalisar, suna kalubalantar kudurin dokar majalisar na hana aike da sakamakon zabe ta intanet.

Daga cikin fuskokin da suka jagoranci zanga zangar akwai tsohon dan takarar shugaban kasa a tutar jam’iyyar Labour Party Peter Obi.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use