Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Shehu Sani ya goyi bayan kalaman Remi Tinubu
Majalisar Dattawan Najeriya ta nada kwamitin mutum 12 don aiki da ta wakilai kan dokar zabe
‘Yan sanda sun kama wani matashi kan zargin sace mahifinsa

Majalisar Dattawan Najeriya ta nada kwamitin mutum 12 don aiki da ta wakilai kan dokar zabe

Majalisar Dattawan Najeriya ta nada kwamitin mutum 12 da zai yi aiki kafada da kafada da Majalisar Wakilai don duba dokar zabe da ake takaddama kanta.

An cimma matsayar ce, bayan zaman gaggawa da majalisar dattijan ta yi da zummar lalubo bakin zare kan bukatun masu zanga zanga a kan dokar zabe.

Shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya ce, sun cimma matsayar ce bayan taba alli da sauran jagorori inda yanzu mutum 12 aka zaba su yi aikin gyaran dokar zaben sabanin 9 da akaso nadawa da farko.

‘Yan Majalisar 12 su ne:

  1. Sanata Simon Bako Lalong – (shugaban kwamiti)
  2. Sanata Mohammed Tahir Monguno – Mamba
  3. Sanata Adamu Aliero – Mamba
  4. Sanata Orji Uzor Kalu – Mamba
  5. Sanata Abba Moro – Mamba
  6. Sanata Asuquo Ekpenyong – Mamba
  7. Sanata Aminu Iya Abbas -Mamba
  8. Sanata Tokunbo Abiru – Mamba
  9. Sanata Niyi Adegbonmire (SAN) – Mamba
  10. Sanata Jibrin Isah – Mamba
  11. Sanata Ipalibo Banigo – Mamba
  12. Sanata Onyekachi Nwebonyi – Mamba

Bayan zayyano sunayensu, shugaban majalisar, Akpabio ya ja hankalinsu da su yi aiki da bangaren majalisar wakilai don samun nasara.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use