Majalisar Dokokin Jihar Ribas ta dakatar da zaman tsige gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyyarsa, Ngozi Odu, bayan shiga tsakani da shugaban kasar Najeriya Bola Tinubu ya yi.
Majalisar ta gabatar da kudirin dakatar da zaman tsigewan a yau Alhamis.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa a zamanta na farko a shekarar 2026, majalisar ta fara zaman tsige Fubara da mataimakiyyarsa bisa zargin aikata manyan laifuka, ciki har da rushe ginin majalisar jihar da kashe kudi ba tare da amincewar majalisar ba.