Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Majalisar Shari’a ta Najeriya ta ce Allah-wadai kaɗai bai wadatar ba kan rikicin Filato

Majalisar Shari’a ta Najeriya ta ce Allah-wadai kaɗai bai wadatar ba kan rikicin Filato Majalisar Shari’a ta Najeriya ta ce Allah-wadai kaɗai bai wadatar ba kan rikicin Filato
SCSN ta yi Allah-wadai da Kisan Angwan Rukuba, ta nemi matakin gaggawa

Majalisar Shari’ah ta Najeriya (SCSN) ta nuna matuƙar baƙin ciki da fushi kan kisan gillar da aka yi wa fararen hula a Angwan Rukuba da ke Jos, Jihar Filato, tana mai kiran gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki mataki mai tsauri domin kawo ƙarshen hare-haren.

A cikin wata sanarwa, majalisar ta ce yawan yin Allah-wadai kawai ba tare da ɗaukar mataki ba ya zama abin damuwa, inda ta jaddada cewa kare rayuka da dukiyoyi shi ne babban nauyin gwamnati.

SCSN ta kuma yi zargin cewa harin na iya kasancewa shiri ne da aka tsara domin tayar da rikicin addini, tare da nuna damuwa kan yiwuwar hannu na wasu ƙungiyoyi ko wasu ‘yan kasashen waje da ke ƙoƙarin haddasa rikici a ƙasar.

Majalisar ta buƙaci a gudanar da bincike mai zurfi, tare da kira ga shugabannin addinai da al’umma su yi aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya da kauce wa tayar da fitina.

Haka kuma, ta miƙa ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Jihar Filato da iyalan waɗanda suka rasu, tana mai kira ga ‘yan Najeriya su kasance masu bin doka da haɗin kai domin hana rikici.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use