Mataimakin gwamnan jihar Kano ya miƙa takardar murabus daga mukaminsa, a wani mataki da aka ce an ɗauka domin amfanin al’umma.
Darikar Kwankwasiyya ta bayyana cewa rikice-rikicen siyasa na baya-bayan nan sun hana ofishin mataimakin gwamnan gudanar da ayyukansa yadda ya kamata, lamarin da ya sa ya ɗauki wannan mataki.
Sai dai ya jaddada cewa murabus ɗin ba yana nufin ya amince da zarge-zargen da ake masa ba ne, yana mai cewa bai aikata wani laifi ba.
Ya kuma bayyana aniyarsa ta ci gaba da siyasa a ƙarƙashin Kwankwasiyya, tare da mayar da hankali kan shirye-shiryen zaɓen 2027.