Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Matashi ya kona mahaifinsa har lahira a Jigawa

Kwamishinan 'yansanda na jihar Jigawa

Wani mutum mai shekaru 60 a ƙaramar hukumar Kazaure ta jihar Jigawa ya rasa ransa bayan da ɗan cikinsa ya cinna masa wuta.

Ana zargin ɗan, Kabiru Nuhu mai shekaru 27, da zuba wa mahaifinsa wani abu da ake kyautata zaton fetur ne, sannan ya banka masa wuta.

‘Yan sanda sun ce ba a san dalilin wannan aika-aika ba, amma sun fara bincike kan lamarin.

A cewar wata sanarwa daga jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandar jihar, SP Shiisu Lawan Adam, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na safe a ranar 1 ga watan Afrilu, 2026, a unguwar Lokon Malamai ta hanyar Magama Quarters a garin Kazaure.

Adam ya ce an garzaya da wanda aka ƙona zuwa wani babban asibiti, amma daga bisani ya rasu.

Yanzu haka dai, wanda ake zargin yana tsare a hannun ‘yan sanda, kuma ana sa ran za a mayar da shi sashen binciken manyan laifuka na jihar (SCID) da ke Dutse domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use