Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Matatar Ɗangote na duba yiwuwar rage farashin fetur

Matatar mai ta Dangote ta sha alwashin sassautawa al’ummar Najeriya Farashin man fetur, a daidai lokacin da ƴan kasuwa ke cewa farashin lita zai iya zarta naira 2,000.

Wannan batu na Ɗangote na zuwa ne bayan da matatar ta sanar da ƙarin kusan Naira 200 kan kowace lita, inda daga naira 995 farashin ya karu zuwa 1,175.

Masana harkokin tattalin arziki na alakanta tashin farasin man fetur din da rikicin kasashen Amurka-Isra’ila da Iran wanda tuni shi ma ya shafi kayan masarufi.

Rahotanni sun bayyana cewa zuwa yanzu ana sayar da kowacce gangar ɗanyen man fetur kan dala 110 zuwa 120 a kasuwar duniya.

Ana dai ganin toshe mashigar Hormuz da Iran ta yi tare da kai wa matatun man wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya hare-hare ne ya haddasa tsadar man fetur din.

Mashigar Hormuz ne ake hada-hadar kashi 20 cikin 100 na makamashin da ake amfani da shi a duniya, lamarin da ke zama babban kalubale idan har ba’a kai ga kawo karshen wannan matsala ba.

Tuni wasu kasashe a yankin Asia suka fara bayyana fargabar samun karancin makamashi, idan har wannan yaki bai kawo karshe cikin gaggawa ba, inda Australia ta ce man fetur din da ke cikin rumbun ajiyarta ba zai zarta wata guda ba.

Ko da yake Iran na duba yiwuwar bude mashigar Hormuz din tare da sanya tsauraran dokoki ga kasashen gabashin duniya.

Zuwa yanzu dai, matatar ta Dangote ta sanar da ƙarin farashin man da ya tasamma 200 kan farashin da ta ke sayar wa a baya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use