Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Boko Haram ta hallaka sojojin Najeriya uku a Adamawa

Wani mummunan hari da aka kai cikin dare wanda ake zargi na mayaƙan Boko Haram ne ya yi sanadiyyar mutuwar sojojin Najeriya uku da wata mace a ƙauyen Garaha da ke jihar Adamawa.

Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa maharan ɗauke da makamai sun kutsa cikin Garaha da misalin karfe 11:00 na dare a ranar Asabar.

Shaidu sun ce ‘yan ta’addan sun isa garin suna ta harbe-harbe domin haddasa firgici kafin su kai farmaki kan sansanin sojoji da ke kusa.

Rahotanni sun nuna bayyana cewa maharan sun ci karfin sojojin lamarin da ya kai suka banka wa muhimman gine-gine wuta, ciki har da makarantar firamare a yankin.

Sun kuma yi awon gaba da makamai daga sansanin sojin tare da ƙwace wata motar sulke, sannan suka cinna wa sansanin wuta.

Shugaban karamar hukumar Hong, Usman Inuwa, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su kara daukar matakai don dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use