Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Ba za mu sa taƙunƙumi kan kafafen sada zumunta ba - Gwamnan Kano
Miliyoyin ‘yan Iran sun yi murna da matakin da Amurka da Isra’ila suka ɗauka a kan ƙasar – Pahlavi
Sojojin Isra’ila biyu sun mutu a Lebanon

Miliyoyin ‘yan Iran sun yi murna da matakin da Amurka da Isra’ila suka ɗauka a kan ƙasar – Pahlavi

Reza Pahlavi, ɗan tsohon sarkin Iran, marigayi Mohammad Reza Pahlavi, ya bayyana cewa miliyoyin ‘yan Iran a ciki da wajen ƙasar sun yi murna da taimakon da Amurka da Isra’ila suka kai wa ‘yan ƙasar.

Pahlavi wanda ya bayyana hakan a wata hirar da ya yi da kafar yada labaran Fox News, ya ce hare‑haren Amurka da Isra’ila sun jawo babban canji a siyasar Iran, inda ya ce sun ba da dama ga jama’a su farka daga tsanantawar gwamnati.

Yariman ya jaddada cewa babu wani tsarin mulki da zai iya ɗorewa sai tsarin dimokradiyya, inda ya ce hakan ne zai ba jama’ar Iran damar zaɓar makomarsu da kansu.

Pahlavi ya kuma bayyana cewa canjin da ake so ga Iran ba wai ya shafi maye gurbinta da wani mutum ba ne kawai, amma ya haɗa da tabbatar da cewa mutane za su iya bayyana ra’ayinsu ta hanyar zaɓe a tsarin mulkin dimokraɗiyya.

Ya ce wannan tsarin ne kawai zai tabbatar da cewa babu wani sabon shugaba da zai riƙa mulki ba tare da amincewar jama’a ba.

Dangane da mahimmancin wannan lokacin, Pahlavi ya ce rikicin na yanzu, wanda ya haɗa da mutuwar Ayatollah Ali Khamenei da wasu shugabanni, ya ba da dama ga ‘yan Iran su faɗi ra’ayinsu kan makomar ƙasarsu, inda yayi fatan cewa za a sami sabon shugabanci wanda zai kawo zaman lafiya da kyakkyawar makoma ga yankin.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use