Fitaccen mai sharhi kan harkokin siyasa, Mahdi Shehu, ya yi gargadi cewa duk wani yunƙuri na kafa mulkin jam’iyya ɗaya a Najeriya zai iya ƙarewa da kunya da kuma rushewar tsarin siyasa.
Mahdi, ya bayyana hakan ne yayin da yake tsokaci kan halin da siyasar ƙasar ke ciki a halin yanzu.
Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya mai inganci tana buƙatar gasa tsakanin jam’iyyu da kuma bambancin ra’ayi, yana mai cewa tsarin jam’iyya ɗaya na hana ‘yancin faɗar albarkacin baki da kuma rage sahihin wakilci na al’umma.
Mahdi Shehu ya kuma nuna cewa tarihi ya tabbatar da cewa ƙasashen da suka rungumi irin wannan tsari sun fuskanci matsaloli kamar rashin adalci, danniya da rikice-rikicen siyasa, wanda a ƙarshe ya kai ga durkushewar gwamnati.
Hakazalika, ya yi kira ga shugabanni da su mutunta kundin tsarin mulki tare da kare ‘yancin jam’iyyun siyasa domin tabbatar da dorewar dimokuraɗiyya da zaman lafiya a ƙasar.
A ƙarshe, ya shawarci ‘yan siyasa da su guji duk wani mataki da zai kai ga tilasta tsarin jam’iyya ɗaya, yana mai cewa haɗin kai ya kamata ya kasance bisa yardar juna, ba tare da tauye haƙƙin dimokuraɗiyya ba.