Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Mutane 3 sun rasa ransu a wani sabon hari a Filato

Mutane 3 sun rasa ransu a wani sabon hari a Filato Mutane 3 sun rasa ransu a wani sabon hari a Filato
Gwamnan Jihar Filato

Mutane uku sun mutu, yayin da ɗaya ya jikkata, a wani sabon hari da aka kai Nyamgo Gyel, Ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu ta Jihar Filato.

Shaidu sun bayyana cewa waɗanda aka kashen suna cikin rukunin matasa kimanin 15 da suke dawowa daga wani wurin hakar ma’adanai a kan babura.

Shugaban matasan Gyel, Dung Davou, ya ce an farmaki rukunin matasan ne da misalin ƙarfe 7 na yamma ranar Juma’a, abin da ya tilasta musu tserewa don tsira.

“Mun fara jin harbin bindiga a nan da can, kowa ya tsere. Abin takaici, mutum uku daga cikinmu sun rasa rayukansu,” in ji shi, yana mai roƙon hukumomi da su ɗauki matakin gaggawa kan hare-haren da ake kaiwa al’umma ba tare da wani dalili ba.

Har izuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba a samu wata sanarwa daga hukumomi kan sabon harin ba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use