Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Mutum huɗu sun mutu a turmutsitsin rabon tallafin Ramadan a Katsina

Gwamnan jihar Katsina Umar Dikko Radda

Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar mutum huɗu a wani turmutsitsin rabon tallafin Ramadan a Kofar-Guga, da ke jihar.

Mai magana da yawun ƴan sandan jihar, DSP Aliyu Abubakar ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya ce an samu kiran gaggawa game da taron jama’a a gidan wani attajiri da ya fitar da kayan abinci domin tallafin ga mabukata.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Bello Shehu, ya miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan tare da addu’ar samun sauki ga waɗanda suka samu raunuka. Ya umarci a ci gaba da bincike da ɗaukar matakan kare faruwar irin haka a nan gaba.

Ya kuma yi kira ga masu sha’awar rabon tallafi cewa su sanar da ‘yan sanda domin samar da tsaro da tsari mai kyau yayin irin waɗannan ayyuka.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use