Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana damuwarsa kan makomar dimokuraɗiyya a Najeriya, inda ya ce ƙasar na dab da komawa tsarin jam’iyya ɗaya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya nuna cewa abubuwan da ke faruwa a siyasar ƙasar na nuna cewa ana takura wa jam’iyyun adawa tare da rage musu tasiri a harkokin mulki.
Makinde ya ƙara da cewa muryoyin masu adawa da wannan tsarin na fuskantar barazana, yayin da wasu ke janyewa daga harkokin siyasa saboda ganin cewa ba a sauraron su.
Ya jaddada cewa dimokuraɗiyya mai ƙarfi tana buƙatar bambancin ra’ayi, jam’iyyu masu ƙarfi da kuma tsarin da ke tabbatar da gaskiya da riƙon amana.
Gwamnan ya gargadi cewa idan aka ci gaba da yin shiru ko rashin nuna damuwa, hakan na iya kai ƙasar ga wani yanayi da zai yi wahalar gyarawa a nan gaba.