Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da tura jakadu 65 zuwa ƙasashe daban-daban da kuma ofisoshin Majalisar Ɗinkin Duniya, ciki har da tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani-Kayode da mai sharhi kan siyasa Reno Omokri da kuma tsohon ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Bello Dambazau.
Sanarwar na kunshe ne a cikin wata takarda da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar, inda ya ce an raba jakadu 31 ƙwararrun jami’an diflomasiyya da kuma 34 na waɗanda ba ma’aikatan diflomasiyya ba zuwa ofisoshin jakadancin Najeriya a sassa daban-daban na duniya.
A cewar sanarwar, an tura Femi Fani-Kayode zuwa ƙasar Jamus yayin da Reno Omokri zai wakilci Najeriya a Mexico. Haka kuma tsohon ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Bello Dambazau zai zama jakadan Najeriya a Beijing na ƙasar China.
Sauran daga cikin jakadun da aka tura sun haɗa da Jimoh Ibrahim wanda aka naɗa a matsayin wakilin Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Olufemi Pedro wanda zai wakilci ƙasar a Australia, yayin da wasu kuma aka tura su zuwa ƙasashe irin su Spain da South Africa da Hungary da Japan da Greece.
Gwamnatin ta ce matakin ya biyo bayan amincewar Majalisar Dattijai ga sunayen jakadun a watan Disamba na shekarar 2025, kuma ma’aikatar harkokin waje ta fara shirye-shiryen horas da su kafin su tafi wuraren aikinsu.