Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Najeriya za ta horas da mutum 300,000 a sabon shirin yaƙi da jahilci

Hukumar yaki da jahilci ta Najeriya NMEC

Hukumar yaƙi da jahilci ta ƙasa, wato National Mass Education Commission (NMEC), ta bayyana aniyarta na horas da mutum 300,000 a wani sabon shiri na bunƙasa ilimi a Najeriya.

Shirin na daga cikin ƙoƙarin rage yawan jahilci musamman a tsakanin manya da matasa a faɗin ƙasar.

A cewar hukumar, sabon tsarin zai mayar da hankali ne kan koyar da karatu da rubutu tare da ƙwarewar rayuwa, domin taimaka wa masu amfani su samu damar inganta rayuwarsu da tattalin arzikinsu.

Hukumar ta ce shirin zai haɗa kai da jihohi da ƙananan hukumomi domin tabbatar da cewa an kai ilimi zuwa yankunan karkara da kuma wuraren da suka fi fama da ƙarancin ilimi.

NMEC ta ƙara da cewa ana sa ran shirin zai taimaka wajen rage gibi a ilimi, musamman ga manya da ba su samu damar zuwa makaranta ba tun farko, tare da ƙarfafa shigar da jama’a cikin ayyukan cigaban ƙasa.

Shirin na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke ƙoƙarin rage yawan jahilci da kuma cimma manufofin ilimi na duniya, inda hukumomi ke ƙara mayar da hankali kan ilimin manya da ƙwarewar zamani.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use