Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama wata mata ƴar asalin jihar Kano da ƙunshin tramadol ƙwaya 3,200 lokacin da take koƙarin tsallaka iyaƙar Seme zuwa Jamhuriyar Benin.
Wata sanarwa da darektan yaɗa labaru na hukumar, Femi Babafemi ya fita a shafin X, ya ce binciken da suka gudanar ya gano cewa matar ta saka ƙwarya a cikinta saboda a ɗauka cewa tana da juna biyu.
Matar mai suna Rabi Muhammad ƴar shekara 35 ta yi amfani da salon cikin bogi don guje wa bincike domin zuwa ta sayar da ƙwayoyin, a cewar hukumar.
A ɗaya gefe, hukumar ta ce ta kama wani ɗan ƙasar Ivory Coast mai suna Michael Gohouri, ɗauke da hodar iblis mai nauyin giram 1.49 lokacin da yake kokarin shiga jirgi zuwa birnin Milan na Italiya.