Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Netanyahu ya ce ana gallaza wa Kiristoci a Najeriya

Isra’ila tayi ikirarin kashe mataimaki na musamman ga shugaban Hezbollah Isra’ila tayi ikirarin kashe mataimaki na musamman ga shugaban Hezbollah
Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu

Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya bayyana damuwarsa kan yadda Kiristoci ke fuskantar gallazawa a Najeriya da wasu ƙasashen Gabas ta Tsakiya, ciki har da Siriya, Lebanon da Turkiyya.

A cikin sakon taya murnar bikin Easter da ya yi wa Kiristoci a duniya, Netanyahu ya ce Isra’ila ce kadai ke kare ‘yancin Kiristoci a cikin yankin, inda ya bayyana cewa al’ummar Kiristoci a ƙasar suna ƙaruwa kuma suna samun ci gaba.

Ya jaddada cewa ko a lokacin hare-haren makamai masu linzami, Isra’ila da Amurka na tsayawa tsayin daka kan Iran da gungun ‘yan ta’addarta, tare da tabbatar da kare ‘yancin addini ga kowane mai bi, musamman a wannan lokaci mai tsarki.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use