Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), ta yi gargaɗin yiwuwar zanga-zangar ƙasa baki daya da kuma kaurace wa zaɓe, sakamakon rudani da saɓanin bayanai daga Majalisar Dattawa kan gyare-gyaren dokar zaɓe, musamman game da tura sakamakon zaɓe ta Intanet.
A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce ƙungiyar na matuƙar damuwa da rashin cimma matsaya kan dokar da aka gyara wacce za ta wajabta tura sakamakon zaɓe ta intanet ko kuma a bar hakan a matsayin zaɓi ga Hukumar Zaɓe ta (INEC).
Kungiyar ta kuma ce samun irin wannan rudanin a lokacin da ake shirin zaben 2027 ba abu ne mai kyau ba.
Har ila yau, NLC ta bukaci Majalisar ta Dattijan da ta fito ta yi wa jama’a bayani domin su fahimci gyare-gyaren da ta ce ta yi.