Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta zargi gwamnatin jihar da yi wa mambobinta bita-da-ƙullin siyasa.
Wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Ibrahim Karaye ya fitar, ya ce abin da gwamnatin ke yi na tsorata ‘ya’yan jam’iyyar ba hali bane na dimokraɗiyya.
Jam’iyyar ta yi zargin cewa gwamnatin jihar wadda aka kafa karkashin NNPP ta fara ƙwace kujerun aikin hajji da ta bai wa wasu mambobinta, ciki har da tsoffin kwamishinoni da kuma jagororin jam’iyya.
Karaye ya ce waɗanda abin ya shafa ƴan jihar Kano ne kuma suna da damar samun kujerun, don haka kada a hukunta su kan wani dalili na siyasa.
NNPP ta kuma zargi gwamnatin jihar da barazana ga tsoffin jami’an gwamnati ta hanyar buƙatar su mayar da ababen hawa da aka ba su lokacin da suke aiki, inda ta kalubalanci cewa waɗannan motoci na cikin alfanunsu na aiki don haka bai kamata a ɓige da siyasa don musguna musu ba.
Jam’iyyar ta buƙaci gwamnatin Kano da ta mutunta ƴancin dimokraɗiyya, inda ta yi gargaɗin cewa saɓanin haka zai iya janyo ruɗani a jihar.