Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta sanar da kafa wata kwamitin lauyoyi domin ƙalubalantar sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a babban birnin tarayya, Abuja.
Matakin na zuwa ne bayan sakamakon da INEC ta bayyana, wanda ya nuna cewa ‘yan takarar APC sun lashe kujerun shugabancin ƙananan hukumomi biyar cikin shida.
APC ta yi nasara a ƙananan hukumomin Abaji, AMAC, Bwari, Kwali da Kuje, yayin da PDP ta samu nasara a Gwagwalada kaɗai. An gudanar da zaɓen ne domin cike kujerun shugabanni shida da kuma kansiloli 62.
Jam’iyyar PDP ta ce zaɓen ya gudana cikin yanayi na karancin fitowar masu kaɗa ƙuri’a, tare da zargin rahotannin sayen ƙuri’u a wasu wurare.
A wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na ƙasa, Ini Ememobong, ya fitar, jam’iyyar ta taya waɗanda suka yi nasara murna, amma ta jaddada cewa akwai kura-kurai da dama a sakamakon da aka sanar.
PDP ta bayyana cewa ƙungiyar lauyoyinta za ta kasance ƙarƙashin jagorancin mai ba ta shawara kan harkokin shari’a na ƙasa, Shafi Bara’u.
Ta kuma yi kira ga dukkan ‘yan takarar da ke da ƙorafi da su gaggauta gabatar da hujjojinsu domin a ɗauki matakin shari’a cikin gaggawa.