Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, ya bayyana kansa a matsayin wanda ya fi cancanta a cikin masu neman shugabancin ƙasa a halin yanzu.
Obi ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan rediyon Magic FM da ke Aba, inda ya zargi gwamnatin tarayya da cewa tana ƙoƙarin hana shi fitowa takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ya kuma ce hana shi shiga zaɓe mai zuwa na daga cikin manyan manufofin gwamnati mai ci.“Gwamnatin da ke mulki na ƙoƙarin ganin ban zama ɗan takara a kowace jam’iyya ba,” in ji shi.
Tsohon gwamnan jihar Anambrar ya ce matsalolin tattalin arziki da shugabanci da Najeriya ke fuskanta na buƙatar mutum mai ƙwarewa a harkokin kasuwanci da gudanarwa, yana mai bayyana kansa a matsayin wanda zai iya magance matsalolin ƙasar.