Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Qatar ta kai ƙorafi ga MDD kan hare haren Iran

Qatar ta kai ƙorafi ga MDD kan hare haren Iran Qatar ta kai ƙorafi ga MDD kan hare haren Iran
Qatar ta kai ƙorafi ga MDD kan hare haren Iran

Ƙasar Qatar ta sanar da aika sabon wasiƙa ga Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, inda ta yi tir da hare-haren da Iran ke kai wa kan ƙasarta.

Wasiƙar, wadda Ma’aikatar Harkokin Wajen Qatar ta fitar, ta lissafa jerin hare-haren jiragen sama marasa matuki da makamai masu linzami da aka kai tsakanin 28 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu, ciki har da harin da ya afkawa wani jirgin ɗaukar mai a cikin ruwan Qatar.

Qatar ta bayyana hare-haren a matsayin “ayyukan da suka sabawa doka” tare da jaddada cewa Iran tana da alhakin biyan diyya kan dukkan asarar da aka samu.

Haka kuma, ƙasar ta nanata haƙƙinta na kare kanta da mayar da martani bisa doka ta ƙasa da ƙasa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use