Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Rasha za ta ci gaba da zama amintacciyar ƙawa kuma aminiyar Tehran – Putin

Vladimir Putin (Shugaban Kasar Rasha)

Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya taya shugabannin Iran murnar bikin sabuwar shekarar Farisawa da kuma murnar shiga lokacin bazara (Nowruz).

Fadar Kremlin ta ce: “Putin ya yi fatan cewa al’ummar Iran za su shawo kan ƙalubalen da suke fuskanta cikin daraja, tare da jaddada cewa Moscow za ta ci gaba da kasancewa amintacciyar ƙawa kuma aminiyar Tehran a wannan mawuyacin hali”

Rasha ta ce hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kai wa kan Iran sun jefa duk Gabas ta Tsakiya cikin haɗari, tare da haifar da matsalar makamashi a duniya.

Haka kuma, Rasha ta bayyana kashe Ayatollah Ali Khamenei a matsayin “kisan zalunci.”

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use