Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Rikicin kabilanci ya yi ajalin mutum 11 a Nasarawa

SP Ramhan Nansel

Kimanin mutum 11 ne suka rasa rayukansu, yayin da gidaje sama da 50 suka ƙone a ranar juma’a sakamakon rikicin ƙabilanci da ya ɓarke a ƙauyukan Akyawa da Udege Kasa, a ƙaramar hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Lafia, inda ya ce wasu da ake zargin ɓata gari ne sun kai harin ramuwar gayya bayan zargin kashe wasu ‘yan uwansu biyu.

Ya bayyana cewa, a yayin harin, an kashe mutum 11, yayin da kimanin gidaje 52 suka ƙone a cikin yankunan biyu.

Nansel ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Shetima Mohammed, ya jagoranci tawaga zuwa wuraren da abin ya shafa domin duba irin ɓarnar da aka yi tare da ɗaukar matakan dawo da zaman lafiya.

Ya ce an bayar da umarnin farautar waɗanda suka aikata wannan aika-aika, tare da tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin, yayin da ‘yan sanda ke aiki tare da sojoji da jami’an NSCDC domin tabbatar da tsaro da dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a yankunan.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use