Rundunar ’yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa mutane 33 sun rasa rayukansu sakamakon wani mummunan hari da aka kai a Gundumar Bui da ke Karamar Hukumar Arewa, bayan wani rikici da ya biyo bayan yunkurin satar shanu da makami.
Mai magana da yawun rundunar, Bashir Usman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce jami’an tsaro sun dauki matakan gaggawa domin shawo kan lamarin.
Sanarwar ta ce rundunar, tare da hadin gwiwar sojoji da sauran hukumomin tsaro, ta tura karin jami’ai da kayan aiki zuwa yankin da abin ya shafa. An kuma fara sintiri na musamman domin dawo da zaman lafiya da tabbatar da tsaro.
Binciken farko ya nuna cewa ana zargin ’yan ta’addan Lakurawa ne suka shiga Gundumar Bui domin satar shanu, inda ake kyautata zaton sun tsallaka ne daga Karamar Hukumar Gudu ta Jihar Sokoto makwabta.
Rahotanni sun ce mazauna kauyukan Mamunu, Awasaka, Tungan Tsoho, Makangara, Kanzo, Gorun Naidal da Dan Mai Ago sun yi yunkurin kare kansu bayan kutsen, lamarin da ya kai ga mummunar arangama da ’yan bindigar.
Rundunar ’yan sanda ta jaddada cewa hare-haren da suka shafi masu dauke da manyan makamai na bukatar hadin gwiwar hukumomin tsaro, tana mai gargadin mazauna da su rika kai rahoton duk wani motsi mai kama da shakku ga jami’an tsaro maimakon daukar doka a hannunsu.
Majiyoyin tsaro sun ce ’yan bindigar sun farmaki kauyukan yankin da ke kan iyaka, inda suka rika bude wuta kan fararen hula ba tare da kakkautawa ba, lamarin da ya haddasa fargaba tare da tilasta wa mazauna da dama tserewa daga gidajensu. A halin yanzu jami’an tsaro na ci gaba da sintiri da farautar maharan tare da kulle hanyoyin da za su iya bi domin tserewa.