Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske
Sojojin Isra’ila biyu sun mutu a Lebanon
Sabon Jagoran Addinin Iran ba zai daɗe a kan mulki ba idan bai samu amincewar Amurka ba – Trump
An samu karuwar sayan makamai a duniya - Rahoto

Sabon Jagoran Addinin Iran ba zai daɗe a kan mulki ba idan bai samu amincewar Amurka ba – Trump

WASHINGTON, DC - MARCH 04: U.S. President Donald Trump speaks during a roundtable meeting on the administration's "ratepayer protection pledge" in the Indian Treaty Room at the White House on March 04, 2026 in Washington, DC. The pledge is a policy designed to shift rising energy costs from artificial intelligence data centers away from consumers. (Photo by Win McNamee/Getty Images)

Shugaba Donald Trump ya ce sabon Jagoran Addinin Iran ba zai daɗe a kan mulki ba idan bai samu amincewar Amurka ba.

Trump a wata hira da ya yi da tashar ABC News, ya ce duk wanda zai zama sabon jagoran addinin Iran dole ne ya samu amincewar Amurka kafin ya kafa ikonsa.

Sai dai Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi watsi da wannan barazana, yana mai cewa ba shugaban Amurka ba ne zai zaɓa wa Iran jagoranta.

A wata hira da ya yi da tashar NBC News, Araghchi ya ce “ba za mu bari kowa ya tsoma baki cikin harkokin cikin gidanmu ba. Al’ummar Iran ne za su zaɓi sabon jagoransu.”

Trump dai ya riga ya bayyana a baya cewa ya kamata ya taka rawa wajen zaɓen sabon Jagoran Addinin Iran bayan mutuwar Ayatollah Ali Khamenei, wanda ya mutu a farkon hare-haren Amurka da Isra’ila da suka fara kwanaki tara da suka gabata.

Rahotanni kuma sun bayyana cewa majalisar da ke da alhakin zaɓen sabon jagoran, ta riga ta gudanar da zaɓe kuma ana sa ran za ta sanar da sunan wanda zai gaji Khamenei nan ba da jimawa ba.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use