Tsohon Darakta-Janar na harkokin yaɗa labarai da Sadarwa ga tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, Salihu Yakasai, ya fice daga jam’iyyar APC tare da komawa jam’iyyar ADC a hukumance.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin, Yakasai ya sanar da wannan mataki bayan tattaunawa da iyali, abokai da kuma abokan hulɗarsa na siyasa.
Ya ce, “Bayan shawarwari da tuntubar iyali da abokai da sauran masu fafutukar siyasa, mun yanke shawarar shiga jam’iyyar ADC sabuwar tafiya, tuni na miƙa takardar ficewa daga APC tare da yin rajista a sabuwar jam’iyyarmu ta ADC.
“Duk masu sha’awar shiga jam’iyyar ADC za su iya yin rajista ta hanyar haɗin jam’iyyar kuma nan ba da jimawa ba za su samu katin zama mambobinta,” in ji Yakasai.