Dan majalisan dattawa mai wakiltar yankin kudu maso gabashin Jihar Rivers, Sanata Mpigi Barinada ya rasu.
Shugaban Kwamitin Ayyuka na Majalisar Wakilai, Akin Alabi, ya tabbatar da wannan labarin a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Alhamis.
Sanata Mpigi, fitaccen dan siyasa ne a Jihar Rivers, wanda aka san shi da jama’a da kuma kakkyawan hulda da ‘yan mazabarsa.
Kamin rasuwar sa, Sanata Mpigi Barinada dai shi ne Shugaban Kwamitin Ayyuka na Majalisar Dattawa.
Ba a tabbatar da cikakkun bayanai game da yanayin da ya faru da mutuwarsa ba a lokacin da aka wallafa wannan labarin.