Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin jinjirin watan azumin watan Ramadan na bana.
Hakan na nufin za a fara azumin daga gobe Laraba, 18 ga watan Fabrairu a ƙasar ta Saudiyya.
Shafin Haramain ne ya tabbatar da hakan ta cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce gobe Laraba za ta kasance ranar farko ta azumin Ramadan.
Ramadan wata ne da Musulmi ke gudanar da azumi. A wannan lokaci, mabiya addinin Musulunci kan kaurace wa ci da sha daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana.