Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Shehu Sani ya goyi bayan kalaman Remi Tinubu

Jigo a siyasar Najeriya, kuma tsohon sanata daga jihar Kaduna Shehu Sani, ya goyi bayan kalaman uwar gidan shugaban kasa Sanata Oluremi Tinubu, na hadaka da gwamnatin Amurka wajen yaki da yan ta’adda a jihar Sokoto, inda ya ce yin hakan zai kakkabe ta’addanci a yankin.

Sani, ya ce ko harin da jam’in sojin Amurka suka kai kan ‘yan bindiga a cikin watan Disambar 2025 ba laifi bane, yana mai cewa, hakan salo ne da dabarun yaki da ‘yan ta’adda.

Sanata Sani, da ya wallafa goyon bayan nasa a shafinsa na X, ya kara da jan hankulan jami’an tsaro, musamman ma rundunar sojin saman Najeriya da su kara kaimi wajen kakkabe ‘yan bindiga a arewacin kasar.

A ranar 25 ga Disambar 2025 ne, sojin Amurka da kuma hadin gwiwa da na Najeriya suka kai hari kan abin da suka kira wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton suna da matsuguni a Jihar Sokoto kusa da mashigar kasar Nijar.

Harin dai na zuwa ne bayan rahotanni sun je wa kasar Amurka cewa ana zargin kashe Kiristoci a Najeriya.

Lamarin ya jawo muhara tsakanin masana harkokin tsaro har ta kai ga fadar shugaban kasar ta tura mai ba wa shugaba Tinubu shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu zuwa Amurka don ya fahimtar da ita cewa harin ‘yan ta’adda a Najeriya na shafar kowa ba iya Kiristoci kadai ba.

Ko dayake a baya bayan nan, Amurkar ta fitar da sanarwar cewa, ta gano ana kashe Musulmai ma a Najeriya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use