Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Shettima ya karbi gwamna Abba Kabir cikin APC a hukumance

Mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima ya karɓi gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf cikin jam’iyyar APC a hukumance.

An gudanar da taron karɓar gwamnan a wani ƙwarya-kwaryar biki da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano.

Tawagar gwamnatin tarayya ta isa jihar Kano bisa jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, shugaban jam’iyyar APC Nentawe Yiltwada da mataimakin shugaban majalisar dattijai, Barau Jibrin da kuma tsohon gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

Da farko dai an tsara karbar gwamnan zuwa jam’iyyar tare da shugaban kasa Bola Tinubu, kafin daga bisani sanarwa ta fito cewa zai kai ziyara jihar Adamawa don kaddamar da muhimman ayyuka.

Tuni dai kallo ya koma kan gwamnatin jihar, da tsofaffin yan jam’iyyar kan yanda zama za ta kasance tsakanin yayan jam’iyyar.

A baya bayan nan ma, an jiyo irin rikice-rikicen da suka kunno kai tsakanin masu biyayya ga tafiyar mataimakin shugaban majalisar dattijai, Barau Jibrin da masu biyayya ga tafiyar tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai ba a hangi fuskar mataimakin gwamnan jihar ba, Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ke biyayya ga Madugun Darikar Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso.

A watan da ya gabata ne gwamnan na Kano ya sanar da komawa APC a wani biki da aka gudanar a fadarsa.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use