Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya fito fili ya musanta zarge-zargen da ake yi masa na cewa yana da hannu a wani shiri na mayar da Najeriya ƙasa mai jam’iyya ɗaya gabanin zaɓen 2027.
Wannan martani na zuwa ne bayan zarge-zarge daga jam’iyyar ADC, wadda ke ganin wasu matakan da INEC ke ɗauka na iya raunana jam’iyyun adawa.
Sai dai Amupitan ya jaddada cewa hukumar zaɓe tana aiki ne bisa doka da tsarin mulki, ba tare da nuna son kai ga kowace jam’iyya ba.