Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Shugaban Iran ya ce zai sadaukar da rayuwarsa don kare ƙasar

Shugaban Iran ya ce zai sadaukar da rayuwarsa don kare ƙasar Shugaban Iran ya ce zai sadaukar da rayuwarsa don kare ƙasar
Shugaban Iran ya ce zai sadaukar da rayuwarsa don kare ƙasar

Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana cewa a shirye yake ya sadaukar da rayuwarsa domin kare ƙasarsa yayin da yaƙi ke ƙara ƙamari.

Shugaban ya ce sama da mutane miliyan 14 a Iran sun nuna shirinsu na bayar da rayukansu domin kare ƙasar, yana mai jaddada cewa shi ma yana cikin waɗanda suka ɗauki wannan alƙawari.

Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da rikici tsakanin Iran da ƙasashen yamma ke ƙara tsananta, tare da barazanar hare-hare kan muhimman ababen more rayuwa kamar tashoshin wutar lantarki da hanyoyin sufuri.

Haka kuma, wasu jami’an gwamnati sun yi kira ga matasa da su fito domin kare muhimman kadarorin ƙasa, abin da ke nuna yadda yanayin yaƙin ke kara tsananta.

Ana ganin wannan mataki a matsayin ƙara zafafa yanayin yaƙi ne, yayin da ake fargabar rikicin zai iya rikide wa zuwa babbar matsala a yankin Gabas ta Tsakiya.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use