Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Sojoji sun kama wanda ake zargi dan ISWAP ne a Borno

Sojoji sun kama wanda ake zargi dan ISWAP ne a Borno Sojoji sun kama wanda ake zargi dan ISWAP ne a Borno
Sojoji sun kama wanda ake zargi dan ISWAP ne a Borno

Dakarun Operation Hadin Kai na rundunar sojin Najeriya sun cafke wani da ake zargi ke da alaƙa da ƙungiyar Boko Haram da ISWAP a jihar Borno yayin da yake ƙoƙarin shiga garin Maiduguri.

An kama wanda ake zargin mai suna Saina ne da misalin ƙarfe 4:42 na yammacin ranar 29 ga Maris a shingen bincike na dakarun 21 Special Armoured Brigade.

Rahotanni sun nuna cewa an same shi cikin mota da farar hula sanye da wandon sojoji, lamarin da ya jawo zargi.

Binciken ya nuna ya yi ƙoƙarin ɓoye kansa a matsayin jami’in rundunar haɗin gwiwa, amma daga baya aka gano yana da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci kuma ana zargin yana kan aikin leƙen asiri.

An miƙa shi ga sashen leƙen asirin sojoji domin ci gaba da bincike.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use