Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Sojojin Najeriya sun cafke wanda ake zargi da yi wa ISWAP leken asiri a Adamawa

Dakarun rundunar Operation HADIN KAI tare da haɗin gwiwar mafarauta da ‘yan banga sun cafke wani da ake zargi da yi wa ƙungiyoyin ta’addanci leken asiri a ƙaramar hukumar Gombi, na jihar Adamawa.

Wanda ake zargin, Abdullahi Umar, mai shekaru 25 ɗan asalin Gwoza, an kama shi ne a ranar 23 ga Maris bayan samun sahihan bayanan sirri kan ayyukan ‘yan ISWAP da Boko Haram a yankin Bataliya ta 232.

Binciken farko ya nuna cewa an tura shi ne domin leƙen hanyoyin shiga sansanin sojoji da wasu muhimman wurare, da nufin shirya kai hare-hare a gaba.

Haka kuma, ya amsa hannu a wani hari da aka kai wa dakaru a garin Ngoshe.

A halin yanzu, jami’an tsaro na ci gaba da tsare shi domin ƙarin bincike da ɗaukar matakan da suka dace.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use