Yanayin Duhu Yanayin Haske
Yanayin Duhu Yanayin Haske

Sojojin Najeriya sun hallaka ƴan ta’adda 61 a jihar Borno

Dakarun sojojin Najeriya na Operation Hadin sun samu gagarumar nasarar kashe akalla ‘yan ta’adda 61 a wasu hare-hare da aka kai a jihar Borno.

Rahotanni sun bayyana cewa waɗannan ‘yan ta’addan na da alaƙa da ƙungiyar ISWAP wadda ke yawan kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin ƙasar.

Sojojin sun kaddamar da hare-haren ne a wurare daban-daban bayan samun bayanan sirri kan motsin ‘yan ta’adda.

An kashe da dama daga cikin ‘yan ta’addan, an kuma tarwatsa sansanoninsu tare da kwato wasu kayayyakin yaƙi.

Wannan ya nuna ƙoƙarin da sojojin ke yi wajen dakile ayyukan ta’addanci a yankin.

Wannan nasara na zuwa ne a daidai lokacin da ake fama da ƙarin hare-hare a jihar Borno da ma yankunan da ke fadin arewa maso gabas.

Samu labarai ta Email

Idan kuka danna maballin subscribe, kuna tabbatar da cewa kun karanta kuma kun yarda da mu. Privacy Policy and Terms of Use